Laila

Laila
Ni ce
Laila
Laila

Gani nazo ki saka ni idon ki (Laila)
Zani furzo kalame daga baki (Laila)
Ki kirani gwarzo a cikin masu san ki (Laila)

Jirgi na yazo Laila (Laila)
Kizo mu keta hazo Laila (Laila)
Zana kai ki muje yawo ki bude idonki a duniya

Laila
Ni ce
Laila
Laila

Babu kowa in gaka kai na hango (Laila)
Zana jingina sai a jikin ka kazama bango (Laila)
In munyi aure kai ne zaka zam bargo (Laila)
Sanka ya ratsa ya shige kashi da 'bargo (Laila)
Alkawarin so mun kulla
Dani da kai ba mai matsala zamu ji dadin tarayya

Laila
Ni ce
Laila
Laila

Tafiyar da na dauko ke zaki min masauki Laila
Sai ki bani ruwa in sha inyi alwalla nai sallah
In daga hanu na sama inta addu'a gun Allah
Ya bani ke muyo aure in kai ki gida na villa
Nai amarya ba kunya
Zanyi shaila (Laila)
In kira su abokai na suzo duk su kwashi tuwo da miya

Laila
Ni ce
Laila
Laila

In da rai rabo ina nan ko watan watarana tabbas
Abinda Allah ya tsara dole zaya faru tillas
Allah tsare dukka wanda suke so saka mini cikas
Watarana zaku dana in saka mashi Pampers
Ni duk wanda yake so na ya bani kudi na rappers
Sai inje kasuwa siyaya
Kawaye su min rakiya

Laila
Ni ce
Laila
Laila

Laila
Ni ce
Laila
Laila



Credits
Writer(s): Trabye
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link