Bako

Bako
Bako
Bako
Bako
Bako
Bako

Sallama mutumcin bako ne
Tunda nayi ku amsa min mutane
Sunana Umar M. Shareef nine
Mai kida da wakar Hausa ne
Garin Kaduna aka haife ni hakkun ne
Gashi na barta kan dalili ne

Bako
Bako
Bako
Bako
Bako

Na fito cikin gida watarana
Zani je studio ma'aikata na
Tafiya nake na rike jita na
Sai na jiyo ana kiran suna na
Wai budurwa ce ta baya na
Sai na tsaya tazo har gaba na
Tace dani nagode Allah na
Yau ya nunan mawaki na
Gari-gari na zo don mu gana
Kwana uku nayi ta yawo cikin rana
Sai tace mini 'Ka bani lamar waya, in koma gida na cika burina'

Bako
Bako
Bako
Bako
Bako
Bako

Ashe, ashe a gida bata sanar ba
Ba tace dasu zata zo gurina ba
Neman ta ake ba inda ba'a je ba
Sai gun aminiyar ta wacce suka saba
Tace da ita Kaduna zata je Habiba
Ita dai M. Shareef take duba
Sai suka dauki motar gida babba
Su kazo Kaduna suka zo duba
Yan sanda dare rana
Kullum dasu ake ta nema na

Na baro asalin mahaifa ta
Iyaye, yayye da kanni na
Masoya masu goya baya na
Nasan suna nan da kewa na
Gani garin da babu dangi na
Nasan da zasu share hawaye na

Bako
Bako
Bako
Bako
Bako
Bako

Taimako a yanzun nake nema
Wai shin wa zai yi mini alfarma?
Ya bani koda makwanci ma
Bana batun cin abinci ma
Nabar wa Allahu mai girma
Lamura na shi yasan dama
Gaskiya fito da ita yan gulma
Su gane banyi laifin ba mai girma
Wayyo ina, wai yaushe zan koma?
Hmm hmm yaushe zan koma?

Nabar Iyaye, yayye, kanne wayyo masoya na



Credits
Writer(s): Lamine Konte
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link