So

Nasan kasan fuskar sa (kai wa?)
Gwaska

Tsun-tsun, tsun-tsun soyayya, soyayya ni dake

Soyayya ni dake
Mun zarce hanta da inji
Kyautatawa tausayi
Gamon jini duka sun hadu

Soyayya ni da kai
Mun zarce hanta da inji
Kyautatawa tausayi
Gamon jini duka sun hadu

Gamon jini, soyayya ce akayi wa kirari
Dani dake kanshi mun hadu
Ba ruwan ta da kyau koko muni
Kun ji tsari, daga zuciya ne ba gudu
Ko ta'ina kin sarkake
Ba yanda zanyi in farrake
Ko'ina naje dole sai dake
Kina jiki na da'iman

Kalmomin so in na furta ta cikin baki na
Ka sani sako ne na zuciya
Tambaya in an min "mai yasa na saka ka cikin rai na?"
Domin kana da kyan halayya
Kana fada mini gaskiya
Ka cire karya a zuciya
Akan ibada ka tsaya
Sannan kuma ka nuna juriya

Nan-nan-nan-nan
Kinga mafarki yayi kamar gaske
Ba hakkun bane
Kan ki nayo don so ya zamo gaske
In nayi hakan zanyo murna take
Don ba sharri bane
Munyo aure ciki dani dake

Ranar da nake jira
Duka masoya in tattara
Za'ayi ruwa har da kankara
Farin cikin mu dole zai dadu

Ka iya baro labari
Wanda suke sa annuri
Idan da cuta kai ne magani
Zuci ta garwashi ruri
Don kuwa kayo tasiri
Soyayya ka gama dani
Ina ta guje-guje
Na rasa shin ina zana je
Kira ni kace min "inzo muje"
Zan bika mu zauna da'iman

Soyayya ni dake (Soyayya ni da kai)
Mun zarce hanta da inji (Mun zarce hanta da inji)
Kyautatawa tausayi (Kyautatawa tausayi)
Gamon jini duka sun hadu (Gamon jini duka sun hadu)



Credits
Writer(s): Andy Sheppard
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link