Na Zaune

Wanda bai yi da mu ba
Ba zai hana mu karbi rabo ba

Wanda bai taba soba
Shi ne na zaune bai ga gari ba, ha la-la

Wanda bai taba so ba
Kira shi da na zaune bai ga gari ba, ah-ah
Dutse a kasan ruwa, bai ma san ana rana ba, ha la-la

Ah-ah, hakika a so wani
Shi kan sa mutum yayi kishi
In da sauran kwana, ko da an ki za'ayi nishi
Tsoron tunkara kara shi kan sa kare yayi haushi
Toh, ku ce da na nesa
Ado Gwanja ke bayan sa ya tsaya
Aya, aha

Sake mu raba, baya yanayi da gyara abinka
Ni banayin gagawa, don sai na aje zan dauka
Amma, mai dan wani naka, take ne da sai hankaka
Ku bani gurin zaman can karshe
Ba na so ku damkan lamba ta daya
Aya, aha

Ku masu ra'ayi na rawa
Kun ga rawar ita wannan waka
Kar ki wahal' da jikinki
Kar ka wahal' da jikinka
Aha

Yi abin da na yi dan neman riba
Sunan sa ciniki
Abin da ankayi domin kyautatawa kira shi da kirki
Abin da ankayi babu zaton sa
Sunansa sauke haki
Zan so na sauke haki
Masun kallo da sauraro nai hadaya
Haba, kai

In ka bani ajeka
Ka hanani inki fadar ka
Dan idan ka mace, na mace
A cen babu amfanin ka
Dan a cen manzo ne kadai
Kai koh kayi ta kanka
Shi kadai mu ka kama
Duk in da zamu ba mai cewa mu tsaya
Aya, kai

Wanda bai taba so ba
Kira shi da na zaune bai ga gari ba, ah-ah
Dutse a kasan ruwa, bai ma san ana rana ba, ha la-la



Credits
Writer(s): Bello Hassan, Ado Isah Gwanja
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link