Ishara

Ishara, ni naiwa miji ya sake ni
Dan Allah laifin da nayo ka sanar dani

Ishara, zaman mu dake ya kare
Kibarni, a garan bawani bayani

Ba tsammani zancen da nake ji gunka
Ya kidima ni idanu sunyo kuka
Bude ni, tina nice matarka
Mai sanka, da mukai auren soyayya

Ishara, zaman mu dake ya kare
Dan Allah laifin da nayo ka sanar dani

Haka rayuwa ke tafiya ba mamaki
Wani yai kwanan titi, wani yai baccin sa a 'daki
Haka yanayin yazo dan Allah karkiyi raki
Na sake ki, zaman mu dake ya kare

Ishara, ni naiwa miji ya sake ni
Kibarni, a garan bawani bayani

Ajizi ne, 'dan adam karda ka 'kini
In naima laifi ni to yafe ni
Laifin da naima ni zanso kaiman bayani
Ko zan rike hujjar da zata raba auren mu na sunnah

Eh kokai da mafari akwai 'karshen sa babu shakka
Albarka, ba zagi kuma ba duka
Dalilin ba sai kinji ba ki daina kuka
Nine na aureki, yanzu kuma na sakeki ganin ra'ayina

Ishara, ni naiwa miji ya sake ni
Kibarni, a garan bawani bayani

To zama dakai zama na lumana
Ladabi biyayya gwargwado na nuna
Da ina cikin jin dadi yanzu kwa 'kuna
Taimaka man, insan laifin danaima mijina

Ishara, zaman mu dake ya kare
Dan Allah laifin da nayo ka sanar dani

Babu tilas ba lallai gara ki barni
Ni gareni ba sauran wani bayani
Zama dake ba bukatan hakan gareni
Abinda nai, a garan yazamo ishara

Minene isharar da ta faru gareka
Nace ki barni ba halin yimaki bayani

Ishara, ni naiwa miji ya sake ni
Dan Allah laifin da nayo ka sanar dani

Ishara zaman mu dake ya kare
Kibarni, a garan bawani bayani



Credits
Writer(s): Sohail Rana
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link