Maryam

Maryama (Maryama)
Wayyo Maryama (gani maryama)
Maryama (Maryama)
Sannu Maryama 'diya da haske
Maryama 'diya da kunya
Maryam mai kyan tarbiyya

Maryama (Maryama)
Wayyo Maryama (gani maryama)
Maryam mariya Maryam
Maryam 'diya ta haske
Juyo in ganki Maryam
Maryam masoyiya ta

Maryama
Nice Maryama
Maryama
Nice Maryama

Maryam karki gujeni
Sam bayake gareni
Mata sun mini muni
In har naganki gabana
Soyayyar ki kibani
Domin in kece raini
Ya zamto babu kamarni
Soyayya in zarce tsara

Maryama
Nice Maryama
Maryama
Wayyo Maryama

Komai kake bukata
Zanyishi ba 'karanta
Na tsaya cak jininda fata
Domin in maka gata
Ni ranka zan faranta
Tunda dai mun samu fahimta
Allah biyan bukata
Alkairi na zuciya ta

Maryam fara ga kunya
Mai ladabi da biyayya
Maryam mai kyan tarbiyya
Banso ki juya baya
Aurenki nina shirya
Nasan baki bani kunya
Mu fara sabuwar soyayya
Idan anka 'daura aure

Maryama
Nice Maryama
Maryama
Nice Maryama

Soyayyar mu gaskiya ce
Da junan mu muka dace
Aure zamuyo mu zarce
Muzamto abin kwatance
Ya Allah kasa dace
A soyayya muyi tazarce
Muyo aure munko dace
Munyo dace da juna

Duhu haske maganin shi
Ya Allah samu cikin shi
Akanka zana nuna kishi
Kokuwa in harbo harsashe
Zan ma kwalliya da 'kunshi
In fesa turare mai 'kamshi
Yazam mijina ba kamar shi
Domin zan baka kulawa

Maryam mariya Maryam
Maryama 'diya ta haske
Juyo in ganki Maryam
Maryam masoyiya ta

Maryama
Nice Maryama
Maryama
Nice Maryama



Credits
Writer(s): Ahmad Jamal
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link