Salon Kida

Daki ruwan salon kida
In muku dan salon na
Naga mata suna dara
Daga ambato na, haba

Bani ruwan salon kida
In muku dan salon na
Naga mata suna dara
Daga ambato na (kai)

Ba'a bugun kalangun mu da sanya, sanya
Ba'a shiga irin gun mu da baya, baya
Rawar kidan mu sai an cire kunya, kunya
Zanso ku gane ganta murhu, tukunya, haba

Da sanu, sanu yaro haka nan ya girma
Ni bani mika hagu baka inda dama
Kyawu ake bukata a cikin makoma
A cikin batun mu bama saka karya, karya, kai

Sauya kama, karki taso da batun baya
Da zare za'a dinke bakin kwarya
Wani yayai rawa an bashi kudi da kaya
Ga wani yayi yaci duka a garin magarya, kai

Daga tirga, sai aka aje jumai
Matsa akayiwa gyada sai tayo mai
Daga gona akan samu firi da mai-mai
Daga tirmi ne akeyin zancen tabarya, haba

Raina kama kaga gaya, ina su Jumai?
Gafa gida da kashe ahu, gidansu Jumai
Alelen gero bariki, kowa takai mai
Ya iya in bai yi ba bazata kai ba, sama

Gwanja na Mai Dawaiya ne ke yin waka
Ni na buga, har nai salon gangar charka
Masu gudu sun tashi, kai ko ina zaka?
Kai yo ambaton kalamanka da gaskiya, haba

Daki ruwan salon kida
In muku dan salon na
Naga mata suna dara
Daga ambato na, haba



Credits
Writer(s): Bello Hassan, Ado Isah Gwanja
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link