Zo Mu Sasanta

Zomu sasanta
Bazamu shirya ba
Ki taimaka min
Nidai kadaina ma bina
Na daina halaye na domin ki na shiryu
Ko babu kai ajiki na nasan da zan rayu
Wai kin mance alkawarin da munkayi tare dake
Ka daina tada min domin ko kayi sake
Sonki zaimin illa karkisa nazamo mai jinya
Banji ina raayin dawo da sonka a zuciya ba

Ahhhh
Zo mu sasanta
Mudaina sa in sa
Na gane inba ke
Bazani rintsa ba
Babu ni babu kai
Ka daina ma bina
Na nisanta da kai
Bazamu shirya ba

Ahhhhhhhh
Ahhhhhhh
Ammmm

Bacci yaso ya kaurace min
A dalilin rabo dake
Gurbinki wa zata mayemin
Banida tamkar yake
Don allah ki tausaya min
Ki jani kusa dake
Mu kore duk gaba
Mu gyara soyayya
To ni ina zanje
Inbaki tare dani
Yazan na tantance
Wazaya damu dani
Kullum a ko yaushe
Hoton ki na nan a kusa dani
Shine abinci na
Sannan kuma shika deben kewa
Zanso ki taimaka min
Ki yafe kurakuraina
Inhar banganki ba
Bazana aikata komai ba

Hmm ka rusa soyayyar
Da zuciya kema
Na daina kaunarka
Zan iya rantsema
Bawata alfarmar
Da zana iya yima
Ka nade tabarmar kunya
Kaje Allah yafema
Mayaudari babu ni babu shi
Tuntini mun raba hanya dashi
Koda da tsautsayi ya gifta
Ni banaso nai gamo dashi
Ka soni kaso kanwata
Raina bazai lamuntaba
Kabar batun soyayyata
Kasan bazakai samuba
Na dau amana nabaka domin na yarda
Bazaka cutar da zuciyata ba haka na shaida
Bawata kalmar da zata kwaceka kai shiru suda
Dani dakai mun yanke alaka bazamu sake ba

Ki taimakamin
Nidai kadaina ma bina

Ehh gaskiya ita kesa mutun yayo kima
Karya kuma nasa a rasa duk dama
Babu ni babu kai matsoni karka soma
Nida yayata bazaka hadamu kishi ba

Ka rasanii
Nima ka rasaniii
Ehhh ka rasamuuuuuu
Ehh ka rasamuuuuu

Salim smart on the beat

Zo mu sasanta
Mudaina sa in sa
Na gane inba ke
Bazani rintsa ba



Credits
Writer(s): Salim Uba
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link