Kina Ina

Wai kina Ina
Kina Ina
Wai Kina Ina
Ni ke nake nima

Kina Ina
Kina Ina
Wai kina Ina
Ni ke nake nima

Tun ran farko da na ganta ni na bata zuciya ta
Buri na ni ta yarje na kirata gimbiya ta
Cikar burin ruhi na kusanci kamar kawa ta
Abokiyar shawara duk sanda nake nema

Wadda zata bani kafada na dora kai na
Kallon farin cikin idonta ke sanyaya rai na
Da ace na rasa ta gara ni na rasa kai na
In ba ita babu ni dan ta zamo jiki na

I'd always love to hear her voice kullum kafin na kwanta
Don't think they'll be a thing da zai sa na daina sonta
Can't see a thing da bana iya yi saboda sonta
Dan ita ce jaruma dan ta mamaye rai na

Ta saka, Igiyar, sonta na ta ja na
Amma yanzu, na rasa, ina ne ta koma
Ina ta buya ne, kodai ta dai a yin so na
Dan ta bar ni da tambaya guda a cikin rai na

Kina ina ne
Ya ki dan ki gane
Kina ina ne
Ina ne zana ganki
Kina ina ne
Kina inaa ne

Lemme take you back dan ku gane me ya faru
Mun hadu ne da ita ne a unguwar samaru
Mukai magana da ita kafin something ya faru

Sai gashi mun yi canjen lamba na ce zan kira ta

Zuwa na gida facebook dina ni na duba
Na tura mata friend request dina domin ta duba
Sai na ga ta amshi friend request dina da na duba
I was happy dan ta bani damar da nake nema

Ni dama mazaunin Kano ne tun asali na
Relationships like this, hardly work a sani na
Amma kuma hakan baya tashin hankali na
Namu was working fine, ni da ita har mun saba

So she'd call me everyday har mu rasa things to say
So I told her za na zo na ganki tell me where you stay
Sai ta ce mu hadu where met, call me in ka ke
Sai na shirya kaya na Samaru ni zana je

Wai kina Ina
Kina Ina
Wai Kina Ina
Ni ke nake nima

Kina Ina
Kina Ina
Wai kina Ina
Ni ke nake nima

Ranar tafiyar I couldn't wait for safiya
After one year dating her yau zan tafi zaria
Ready to see masoyiya har mu rabu lafiya
Amma da na je na kira wayarta ta ki shiga

Ban tada hankali ba dan hakan na faruwa
I thought bata da caji dan jiya an yi ruwa
After hours na kira na ji me yake faruwa
Her phone was still off hakan ya sa ni damuwa

Bayan anyi hakan sai na fara bin mutane
Ina ta musu tambaya, bayani dan su gane
Yanzu anyi shekara, ita ko tana ina ne
Ta bace, totally, ba ita ba labari

Na yi wannan wakar ne, ko zata ji ni
Ko za a samu wani ya kawo mun bayani
Fata na daya, ubangiji ya taimake ni
Dan na fa haukace a santa ban iya nishadi

Kina ina ne
Ya ki dan ki gane
Kina ina ne
Ina ne zana ganki
Kina ina ne
Kina inaa ne



Credits
Writer(s): Yusuf Muhammad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link