Ruwa Ya Girmi Gwani

Ruwa ya girmi gwani
Kasa sirrin magini
Tsakanin dan Gwanja da mata Allah masani

Musax beat

Kura kin kori kare amarya kece da zare
Dan dai aure baya raka aure da za ki dani

Eh idan kunji gurbin zama da tirmi sashin daka ne
Da ance gaya na biyunsa kowa yasan kwado ne
Da ance ciza gaza da tauna aikin baka ne
Shi kam daukar kai har da kaya aikin wuya ne
Kura ta dau fara ta nuna ribar kafa ne
Sai an mance baya zahiri sanan za'a gaba

Sama sama sama
Eh-hh-hh-hh-hh-hh

Idan har anso kiyi kuskure sai an dinga kula
Da kin taka hauni ki taka dama a kara kula
Kije hagun da dama gaba da baya a kara kula
Da kinyi kuskure karami ace miki kin zagi Bala
Da Allah ya kaiki ga matsayi sai kin kara kula
Misalin mata ba kowani tarko zai cin muku ba

Kai girgiza maza juya
Karkada maza juya
Ku gwada musu kun shekara lafiya

Sama, kai, aha
Haba, kai
Horibo, tir, sama mata

Kai, haba
Sama, horibo, kai

Kowa yasan mune da mata sune fa da mu
Ansha bakar wahala a baya kafin a gamu
Kullum kukan gwada duka zakin sautinku ga mu
Kullun fada mata da duk wanda zai taba mu
Da wanan nake dada gane cewa kun gamsu damu
Idan dai har na zaga wani guda bazai ki muku ba

Kamar kwai yakan gwada kyau a fili aikin farali
Ba lalai ace ciki nada kyau ba kar kuyi gatsali
Wani yace nace sama dai ga mata an hau shagali
Da jita taba da kilinkili mata sun karbi ali
Maza ma ku juya in zaku juya ban san fi'ili
Ku hau saho ku daina fada da mata bazai muku ba

Tsakanin dan Gwanja da mata Allah masani

Musax mix



Credits
Writer(s): Ado Isah Gwanja
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link