Soyayya

So na ne fah
On the beat

Soyayyar ki ce take mani yawo nidai
Kabani labari
Rayuwa tana son sirri sai dai
Ka furta alkhairi
Komai nawa sai kina nan zayai dai-dai
Kana da kyan tsari
Da zanai fushi da mai suka amman dai
Ka jure yin tari

Dukkan wani babban ba ya rike girma
Kace da shi yaro yake
In har rai da lafiya bama gaza nema
A zuci tasirin yake
Kin kana ganin ka toh kai mai jarkoma
Ruwan iya gwiwa yake
Shin an tashi lafiya sanadin hadin gulma
Batun da in yanke yake
Toh juya ki rausaya sai kin mini tsalle
Gaban ka zan taka

In ba ni ba kowa taho ki masa kwalele
Ka daina yin shaka
Zan goge gumin jiki na zan dada kyale
Ka ja ni zan bika
Kauna ke tsuma bana san sada tale
Kawai muje harka
Toh ya kinka tashi bacci dazu da safe?
Ina tunannin ka
Daure sa kai batun batun kar ki mini yarffe
Ya zana ma haka?

Kauna bata goguwa koda an tsufe
Batun ka ba shakka
Sirrin zuci yanzu zam bude shi a faife
Ka kyale mai suka

So a so ka magani
Jani a son na kwantar hankali
Da akwai rabo mai kallo zai taka dandali
Kauna ta shige cikin zuciya
Ta zauna da kyalkyali
Wacca nakewa so tanai min so mai kyawu da tozali
Ka san yau da gobe sai Allah dan shi ne da zamani
Na yarje a bangaren soyayya nidai ka tai dani
Bana tantama ina sonka kawai ni dai kula dani
Kar watarana ni da kai mun saba kai mini lahani

Na gane matsalar
Ni ma matsla ta ce
Na gane maganar
Ai nima magana ta ce
Rike ni muje inuwar
Kai din ai kadara ta ce
In har nayi kira sa kune saurari kalamai na
Jirgin za ya cira Allah na iya maida dare rana
Kyautar so ki rike zo karbi flower a hannu na

Bini da kauna
Ni kuma sai ki gwada mini soyayya
So da amana na dau alkawari
Ya zan sauya?
Kar kaji zance
Soyayyar ka ce take yi mini yawo
In naga ba ke a kusa dani abun nai mini ciwo
Kai ni misalin soyayyar ka a rai na na dauka
Na biya allo dukkan wani karatu na dauka

Mixed kobincus



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link