Ghana Most Go

So na ne fah
On the beat

So in akwai riya ko an kula shi baya yin karko
Kuka na zuciya ban san ran da zaiyi karshe ba
Kin yaudare ni yan mata

Komai nake fada tabbas baza na huce haushi ba
In damina tazo nasan baza a rassa raba ba
Zan dauki kaddarar so ne baza na maki komai ba
Kin sauke alkawar wanda mukai har gaban yi nema

Tamkar bana gani bana ji na tai kai ruwa rana
Samun ki ne kawai shi zai zamto cikar muradi na
Sirri da naki ne kinsan komai da ke cikin rai na
Ni so na gaskiya nai maki ban taba miki karya ba

Har kin manta lokacin da bana manzgon ki kika zo birni
Wai yanzu kin kile babu abokin fadan ki sai dai ni
Karshen munafuki jin kunya jeki ba ruwana ni
Zaki da na sani amman nidai ban maki fata ba

Tsintaciyar mage anka ce bata mage na gano
Idan naji sirrin kan nan da kike boye mini an tono
Allah bamu lafiya ni na aure wutar da kin kunno
Na gode rabbi ban zama kaza mai ci ta goge baki ba
Nan zana barki yan mata

Dubi kalar ki kowa sai dada kauna yake
Kin yi kibar ki nikuma sai dada rama nake
Banda ta cewa tunda hakan kaddara ta take
In banda kuka zuciya bansan mi zanyi ba

Kin aje kauna zaki biye rudin duniya
Kin mini barna zuciya amman ya na iya
Ya kika so nayi akan ki dan aka min tambaya
Nayo tunannin sai dai in mutuwa ta raba
Nan zana barki yan mata



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link