Dama_Ace

Ace muna tare dani dake aminiya
Da zuciyarki zan wake kibar fishi masoyiya
Ga shawari ga maiyin so karda ya dinga zuciya
Duk inda so yai tasiri dole akwai dawai niya
Bazana bar bayanai ba saikin bani soyayya
Arai baxanji dadi ba in kin barni kan hanya
Wai meyasa dana ganki guiwowi suke karaya
Tabbas kina da kwarjini kulaki sai an shirya

Rubuta sakon ni amma nakasa tura wa
Nasha shirin fada miki amma nakasa furtawa
Har alumma suna cewa wai ya naketa karewa
Ban rasa ciba balle sha amma inata ramewa
Kece kadai tunani na cikin dare xuwa rana
Ido ina ganin yana dan allah ji tausai na
Bara nake ki kalle ni hannaye da koko na
Kice dani kina sona shi xai share kuka na

Ni dukka nin kalamai na saboda ke na tsara su
Ki karbi duk bayanai na a kasa karki yada su
Kibani dukka sirrin ki wallahi bani tona su
In babu ke a soyayya xa'a kirani susu su
In kika soni yan mata baxana sake kalla ba
Ko sun bani kyauta sam jameel baxana karba ba
Zanso ace muyo aure dani dake muhau turba
Mu kulle dukka nin kyaure da godiya gurin Allah



Credits
Writer(s): Don Shuwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link