Banida Kowa

Ahh banida kowa
Nima banida kowa ni sai kai
Ahh bani kishir ruwa
Nima bani kishir ruwa ga don kai
Ahh bani gazawa
Ahh nima bani gazawa domin kai
Ahh bani gujewa
Ahh nima bani gujewa haka dan kai
Ahh zana iya wa
Ni bani da limami sai kai

Ahh dan na fakewa
In kwana fakewa ga dan kai
Ahh dan na iyawa
Na bada tasawa ga dan kai

Abun da nai barbada dan sanki nake
Kigane muradai na
Indai na jingina kallonki nake
Ki damke mukamai na
Inda nai gardama da in barka nace, "A shafe misalai na"
Adon zama laluma kallonka nake na wanke idanu na

Ahh, ba min jiniya ta keki nake
Dadin duniyata ta kai
Zamin igiya sunan ki take
Taka lafiya dan ka kai
A talayan gardama bayan ki suke
Kanka sai inga karshen dambe
Duk dan abun duniya dai dan ki nake
Ko kai ba a sani a ranbe
Ga halayyar ki ma ta bada gami
In ka tanka ni toh na kara tsimi

A dan karatu na allo sai da gwani
Chan cikin zuciyata kai naiwa kwami
Abar abun tunhuma na miki hani
Kai ka gyaran zubin kwana da wuni
Ahh, ga kauna bani kauna, ha, ha, ha, ha, ha
Lallube bai biya na, ha, ha, ha, ha, ha
Tallafa bani kauna, na gane
In na bude idona, kallonaka ne
Sananan nufi na kin gane shiru bai biya na zance ne
Fada ban ki bi ba, karya ne

Kanka ni ban musu ba, anyi zane
Da zaran ka sauka cikin tawaga ba mai ziga na ka nane
Ahh ina mai fadin mun zame?
Ahh mun sha ziga mun jurai
Da kwai mai fadin ya tonai
Da ya yau zubi mun zamai
Ahh mai abun fufuka tuntu ne
Kashi ke rufe bargo
Mai bida ko yana samko ne
Da sa'a yake koli ne

Asalin mai jidan kaya ne
A kama ya ce dadi dai ne
Da ya runguma ya kasa barai ya ishe shinginsa

Ha, ha, ha, ha ina mai biya na ha, labari?
Da ka ambata yai tasiri
Gani nan gaki toh wani ya kasa, wani ya kasa
Ga kwarai tafiyar dada tayi nisa, wani ya kasa
Da kyan aniya mun kai laya
Da kyan aniya mun kai laya
Ahh dan da kyawun niyya mun kai niyya
Da kyawun niyya mun kai niyya
Mai abun ai fadi sai an tona
Ai yanzu shairri ka sa wasu ke jinya

Mixed kobincus



Credits
Writer(s): Muhammad Yunus
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link