Muradin Rai

Cikar muradi na
Kai ne cikar muradi na
(S piano on the beat)
A kai ki daki na
Ni kuma ka zama ango na

Gefen ki zan zauna
Zo karaso mu tattauna
Kina cikin rai na
Nima kana cikin rai na fah

Cikar muradi na
In babu ke ina zan kwana?
A zuci kin karbo
Bana da wata in bake ba

Nidai ka ban zumar kauna
Sannan ka kama hanaye na
Cikar muradi na bana da wani in ba kai ba
Bana da wani in ba kai ba

Iya muradin rai shi ne abashi zabin sa
Tunda shi so bamu gane abun da ya kunsa
Zuciya sai in kin raye zata numfasa
Ke kadai ce har ila yau ban canza layi ba

Duk ran da na waiga idan ba ka zana susuce
Tunda namiji garkuwa ne a gun diyya mace
Na amince bana canza ka kai na tantance
Kaga shi so bai da zabi bai san adawa ba
Ni dai ka kama hannaye na

Wanda ya so ka so shi dan Allah kuji dadin rayuwa
In na same ki zuciya ta bata da sauran damuwa
So da dadi dani dake bani fatan rabuwa
Duk abun da zai zama bacin rai gunki ni bazan yi ba
Yau rawa ta zanyi nayo juyi gani ga sabon jini
Ra'ayin zuci aka ce so kai wa sa'o'i kwarjini
Ka kadai ne na ba makule na zuciyata ba wani
Wanda zai ce na barka lallai jinin mu bazai jitu ba

Cikar muradi na
In babu ke ina zan kwana?
A zuci kin karbu bana da wata in ba ke ba
Ni dai ka ban zumar kauna
Sannan ka kama hanaye na
Cikar muradi na
Bana da wani in ba kai ba

Bana da wani in ba kai ba



Credits
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link