Kujerar mata

Kujerar tsakar gida
Wajen zama na mata
Wacce duk ta hau taga miji, taki tafi sara

Sama
Ehh
Kai!

Nace, "Kujerar tsakar gida"
Wajen zama na mata
Banda mai duwawu
A kasa-kasa kamar na kura

Nace kar kuce in kwanta
Dan ba bacci nazo ba
Kar kuce in tashi
Baku ganni da fuka-fukai ba
Karku kaini idan ba zaiyu in fito ba
Gangar kidin ta mata ce ba maza ba (Sama)

Allahu ya nufa yauma gani nazo
Ku dauro bazar rawarku kumbu na murzo
Idan ana dara uwa aka so aka tazo
Ni da uba nike ado ba da rigar aro ba

Wata tana rawa da takun ta da baya-baya
Ba dake nake ba balle kice nayi karya
Kowa yaja da ikon God zaiji kunya
Kan wani yayi mani jiri na karya
Baku sha ruwa ba (sama)

Nasaba in naje gidan biki ince
Yan mata aje sama
Ince mata aje sama
Ince mata aje kasa
Ahh-ahh-ahh
Kai
Eh
Toh

Ga kirjin bikin gurin nan, naga tazo
Ba wanda zaya ce yazo shi bikin yaci kanzo
Naga yan maza a wajen harma mata sun zo
In baku na kan ce banga kujerun gida ba

Matan gidan ga dai taku kun iya
Kuyi rawa-rawa nace kar naga kun tsaya
Kuyo takun ku dan ku gagara kwaikwaiya
Ita waka akan buga ma ku ba dan kudi ba

Cigaba na maigida-gida
Shi ya guji gobara
Na tafi zan barku
Karku ce na fiya gun dira
Kujerar tsakar gida
Wajen zama na mata-aa-aa-aa
Na mata

A'a na mata
Sama
Ehh
Toh-toh-toh

Kujerar tsakar gida
Wurin zama ma mata



Credits
Writer(s): Bello Hassan, Ado Isah Gwanja
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link