Share ido amarya

Share ido ki bar yin hawaye amarya
Sha kurumin ki angon ki ne, kunyi aure

Da fari makaki Allahu na sanya a farko
Wanda yayo shekara, yayi wata, yayi mako
Dafa min Allah in sauke kayan dana dauko
Na hangi amarya da ango yau take ranar aure

Gida zaki je, haba-haba amarya
Bikin naku ne, ki bar masu karya
Ki dau shawarar iyaye amarya
Ki mance zugar kawaye a baya
Haba-haba amarya mai ladabi biyyayya

Ki bi sahun mijin ki
Amarya kiyi dauki
Dan aljannaki
Tana kafar mijin ki
Rike hannu mijinki amarya ku tafi tare

Naga daso a cikin sha'anin nan
Har ta kai su ga aure
Taci ado da asoke amarya har ta fesa turare

Ki damke mijinki
Shine jikon ki
Ina makusan tan?
Ku zo kuji zancen
Rawa da alantan
Da ni muku rance
Waka da salon da yake taba zuciya ta amare

Sha'anin aure riba ce
Kin zama dauko riga
Kin zama dauko hula
Amarya dauko buta
Toh ki sani aure bauta ne
Babu fushi a zaman ku na kauna
Amarya-aa-aa--aa-aa

Amarya zauna
Ga nan ku na tura
Mun tayaki da murna
Biki naki ake amarsu daure, daure
Toh haka, haka

Zo ku ji zan ce daga bakin Ado na gwanja
Ni na karanta na nazarta kuma ina da hujja
Aure nasara ce nasaba ce ba jani in ja

Waka ado nake
Sana'a ce na rike
Da kai nake har da ke
Baiti in nai rike
Bana daki in dake
Gumina ci nake
Ban yarda a bi in tare

Kama dai da wane ba ta wane
Bikin yau na zo ina mata ne?
Ku bude jakar kari daidai ne

Gaku nan ga amarya
Ga angon amarya
Ga mawakin amarya
Ina kawayen amarya?
Abokai ku shirya
Gaku nan ga amarya
Kuyi rawa ku juya
Ayi gaba ayi baya
Kuma ku fidda kunya saboda ga amarya

Albishirin ki yan mata albishirin ki
Tashi ki juya kiyo rawa da bazar ki
Na gano yan uwa da dangi na san ki
Albishirin ki amarya ahir din ki
Dauki tsararun kwarai cikin su kawayen ki
Dan gudun karsu kai ki can haka su baro ki

In ki kai haka sai muce kin ci garin ki
Kin zama tilo cikin su kawayen ki
Ba tambaya da ganin ki kinci sunanki
Kiji ki kiki ji, ki gani ki rintsa ido amarya



Credits
Writer(s): Bello Hassan, Ado Isah Gwanja
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link