Meerah

Na tashi dake
Zuci yau ke zan wa baituka na
Farar aniya
Suna gimbiya
Allahu yasan manufa na
Iya yanayin
Dana damu dashi rai ya zan na manta

Baiwar Allah
Hasken fitila
Mai haske cikin bakin gida na
Na rayu dake
Rayuwar da ba zaiyu na manta dashi ba
Cikin natsuwa
Akai shakuwa
Ra'ayin ki yazama ra'ayi na

Kin tashi da kyau
Tsarukan ki akai ba zanyi tantama ba
Kina da Hali
Sannan asali
Koyi da ake da dan Amina
Samun ki cikin
Dubu na dubu na mutane ban tabbatar ba
Akwai natsuwa
Ta sani tsuma
A dole na sunkuyar da kai na

Kyauwun ki
Halittar ki
Muryar ki
Dasu na cire bakin ciki na
Ina fahari
Na tare dani
Kina ciki yar cikin gida na

Meerah diya mai dubun alkhairi zuciyar ki babu cuta
Kina da aji
Suma daga ji
Sun san an tashi duk amo na

Ni fah bazan manta ba
Ban zatan zan koka ba
Wai ashe ban dace ba
Tunda dai ban dafe ba

Da mai share hawayen ki in sun ka zuba
Tausayin da nake ni
Wa za ya taya ni?
Sarautar ki, matsayin ki bazai tabu ba
Kinyi daban a mutane
Samu ya wuce ni

Ameera na san ko ba kwalliya fuskar ki da kyan halitta
Sa'a da rabo, na kanyi yabo, in tayi abin bajinta
Duk wanda yai sa'a da samun ki a zuciya baya cuta
Wanda yayi rashin ki duniya shin ina zai je ya huta?
Iya tsanani, laifukan ki Ameerah ba zaiyu in gani ba
Na kan kore shi in na tuno matsayin ki a zuciya na duba
Komai sanadi akasi da ya zo sam-sam bai kore mafita ba
Abinda nayi nufi, na barshi a rai na ba zan furto ba

So ya kan nuna kamanni
Da a can bai burge ni
Ba zato ba tsammani
Tausayi ya kama ni

(It's Hassan the youngest producer)



Credits
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link