Kiyi Hakuri

Dan Musa yazo da waka
(Bayo)

Bin ki nake ina ta roko don Allah ki yafe laifin da nayi miki
Ko ba don ni ba don yaran ki kizo ki dubi halin da muke ciki
Dawainiyar uwa ga yaranta da dukka hakki ne kika bar mini
Komai nake yi ya gagara bani iyawa kiji na sake hali

Farin cikin aure yanzu dai ban samu ba
Bani blaming kowa kullum sai dai kai na
Wanga hali yasa ni kamar naji inyo hauka
Aure in ba'a sasanta ba, bai kyautu a rusa ba

Kiyi hakuri, don Allah karda ki kama ni da laifi
Kiyi hakuri, abin da nayi bazan sake miki ba
Kiyi hakuri, don Allah karda ki kama ni da laifi
Kiyi hakuri, abin da nayi bazan sake miki ba

Oh-ooh-oh-hoooh-oh hoo-oh-oh
Eyee-yee-yee-yee-yee-ye-ye-ye
Komai ma in ba'a yafe ba
Toh da ba haka ba
Da kowa yanzu yana daure, yarin prisoner

Ban ce ban miki komai ba, ni na yarda da laifi na
Da hukunci kika min kema, ni na horu ko na tuba
Naga wata da fitar rana, ban iya rintsa idanu na
Tunda nace miki na tuba, toh na gamsu ne da laifi na

Wani hali mara dadi ne oho, ya birkita mini tsari na
Dama ki dawo muyi miki oyoyo, dani da yara, da makota
Zama ace babu ke na tenono, ba dai dani za'a yi shi ba
Yaushe zaki dawo mu dinga chapter dake? Don na jima fah banji ki ba

Kiyi hakuri, don Allah karda ki kama ni da laifi
Kiyi hakuri, abin da nayi bazan sake miki ba
Kiyi hakuri, don Allah karda ki kama ni da laifi
Kiyi hakuri, abin da nayi bazan sake miki ba
Kiyi hakuri, don Allah karda ki kama ni da laifi
Kiyi hakuri, abin da nayi bazan sake miki ba
Kiyi hakuri, don Allah karda ki kama ni da laifi
Kiyi hakuri, abin da nayi bazan sake miki ba

(Bad Mix)
Oh-ooh-oh-hoooh-oh hoo-oh-oh
Eyee-yee-yee-yee-yee-ye-ye-ye
Komai ma in ba'a yafe ba
Toh da ba haka ba
Da kowa yanzu yana daure, yarin prisoner

Credits
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link