Rgm

Dan Musa yazo da waka
(Prince Production)

Masoyi yana da rana
Ko babu komai shine ka debe kewa
Kamar dai kace ashana
Sam bashi wuta sai da taimakon makyasta
Ko ranar da babu dadi
Sai masoyi kadai ke taya ka kuka
In kayi rashin masoyi
A kiyasi ka rasa bangaren jikin ka, oh-hoho

Ranar ganin masoyi, a rayuwar nan ni naga ba irin ta, la-la-la-la-la-la
Allah ka ban masoyi, da zai iya hakuri da duka halika na, la-la-la-la-la-la
Nasan na kanyi laifi a hukunci bai wuce kuruciya ce ba, la-la-la-la-la-la
Allah ya barmu tare, in mun mutu ma a Aljannah muyi zumunta, la-la-la-la-la-la

Ni ba ilimi ba
Ba kudi ba
Ba wani kyau ba da za'a rangwada ma
Ni bani da kowa in ba Allah ba
Da yayi mini rai na da lafiya na
Haka shi ya tsara, in daga murya ta, inyi maku waka maganar cikin ciki na

Ku so, ku so, kawai ku so masoya
Ku so, ku so, kawai ku so masoya

Ranar ganin masoyi, a rayuwar nan ni naga ba irin ta, la-la-la-la-la-la
Allah ka ban masoyi, da zai iya hakuri da duka halika na, la-la-la-la-la-la
Nasan na kanyi laifi a hukunci bai wuce kuruciya ce ba, la-la-la-la-la-la
Allah ya barmu tare, in mun mutu ma a Aljannah muyi zumunta, la-la-la-la-la-la

(It's Prince on the mix)

Credits
Writer(s): Musa Muhammad Dan Musa
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link