So Ne

S piano on the beat

Shi so mai tajin launi
Ka saman ba tsammani
Garin mu ana ce dani na zama sadauki
Kece dani yau naki
Nima kaina na baki
Aminta dani kar ki sare baby kira ni

Akanki na zama makaho
Wa'yansu sunai mini ihu
Sillar kauna zuci al amarin ba sauki
Sam bana ci bana sha
Nazama tamkar sha-sha-sha
Na tabbata so baida karshe ko a ma'auni

Shi dai sha'anin soyayya
Yana sa ayi tarayya
A kasa fahimtar miye ma ke a tsakani
Suna sa rai ya fusata
Sular haka har ya dimota
Nagane so bai da tsadar wani ma zauni

So baida gwani nayi auni
Yana hana rai sukuni
Hawan shi da kyal za ayo sauka da tunani
Shi dai lokaci bako ne
Idan har kazama wane
Sai an tabbata kagane karkara har birni

Shi so mai da gula harka
Ba wanda ya sa shi a fuska
Sanin shi wuya dan danon sa zuma ko daci
Akan rasa kan soyayya
Wadansu su sa suyi jinya
Ana hauka sanadin so ayi maraici

Mai so baya da dubara
Baya lura da asara
Ya kan zautu har ya sanya wadansu takaici
Sharrin so in zai fara
Baya duba ka tara
Ya ka rutsa mai shi da mai neman na abinci

So ne ke sanya farauta
Ka naji kayi ta wahalta
Da an magana sai kace so sai da azanci
Dare ya zamo mini rana
Kina ta gizo a ido na
Da na kwanta damuwa sai in shiga kunci
Ku min uzuri zan furta
Duk mai so kar ya kagawta
Domin shi so asali ba sabo ne ba

Mix kobincus



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link