Budurwa

Baby
I love you
Zo muyi soyayya
In so yayi so
Bai uzuri gaskiya?
Kina nan a rai
Wallahi ba tsakiya
Cikin zuciya kin zama tilo daya
Baby zani so
Ki min rikon gaskiya

Indai kanki ne
Ni bani ji ban gani
Soyayyar ki tazama turuwa har jini
Gidan duniya
Ai kinyi min an gani
Mai kyawun gani kinyi wa maza kwarjini

Kauna ta rufe
Na san so ya fito
Ko bacci nake
Ke dai nake ambato
Idan babu ke
Na tabbata na mato
Zumar so da kauna
Na sha ina walwala

Rabin rayuwa wallahi kin zama gare ni
Idan na kira mata babu mai mini raini
Budurwa, soyayyarki ni ta shige ni
Kyakkyawa, fit'sarin suffar ai bayani

Zan so ki sani
Ba ke bazan rayu ba
Rike alkawar'
Ki rike bama rabu ba
Idan na rasa ki
Ba zan bar kukan zuci ba
Soyayyarki ce jari
Bazan bata baya ba

Ashe zuci ma amsa ma ruhi amo
Sullar shakuwa fansa guda mun zamo
Akan so da kauna daga kanki na sallamo
Cikin zuciya kece na baiwa mulki
Gidan duniya mata garen ba kamar ki
A kwalliya sai mata su koya gareki
Baby, halayen ki na sani shawki
Ki shayar dani tsantsa ta so yar uwa
Akwai ilimi a gareki ga natsuwa
Kaunar gaskiya kin mini ba damuwa
Taya za a ce ba zan mutunta ki ba?

Budurwa
Baby
Budurwa
I love you



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link