Rufa Ki Saya

Kin ratsa zuciya, a duniya in bake ba Sani
Kar ki tayar dani, masoyiya a rai ki sanya ni

Kaunar ki ta zaman tamkar ruwa na sha ji tausayi na
In bake duniya, a bangaren so wa zaiyi jin kai na?
Ni bana so a ce, "Dani dake zamu furta bankwana"
Na baki rayuwa, fanni na so kin kure tunani na
Kinsan so a zuciya bai zama duk inda zaya samu zafi
Zan fada a rijiya, gaba dubu kanki ban ganin zurfi
Ki saurari zantukan, so aka ce mai hana ganin laifi
Shi mai so majinyaci ne, a koda yaushe bana mai yafi
Kiban gurin kwana

Hasken idaniya, kin zam gare ni gun ki ban karya ba
Na duba nahiya, mai kyan siffar ki wallah ban samo ba
Zo kada ga kujera, zuciyata na baki zauna
Komai kike bukata, fade shi zan iya yi da kaina
Na kulle zuciya ta wake kadai rabi na raina
Hasken dake cikin zuci ke sila ce iya sani na
Na toshe dama, na toshe hagu kece na baiwa kauna
Nidai biyan bukatu na zuciya ki zana sunana

Na baki zuciya, masoyiya daure ki yanta ni
Duk inda zana je, saboda ke ana mutunta ni
Nina fake dake, kowanda ya ganni zaya ce Sani
Silar ki zan zama ta wane daure rufa ki saya ni
Ni ban gudun ace, akan ki na zama mai karambani
In kin guje mini, kisa a ranki zan shiga rudani
Duk wanda zaya zo gare ki, daure kice dashi sai ni
Ranar farin ciki, gare ni shine dake muyi aure

(Mix Golden Ghost)



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link