So Makaho Ne

Mafarki na, kece

So makaho ne
Naga baya gane dan gida
Bai gani bai ji
Bai gudun ya rufta gargada
Masu jirwaye su suke gudun sawkar kuda
Hadarin kauna ai kina jin yau karar cida

Gaskiyar zance
Sanki ya taba min zuciya
Mai gani ga kyau tafiyyar ki daya bayan daya
Zan zamo bawa korafin ki bana firjiya
Duk abun da kike so ki ban umarni zan iya
Murmushin kauna
Kiyi a gare ni in san mafuta
Ai idan gaki da wajen ne ya zando wuta
Tunda zafin so ya darar wa garwashin wuta
Yaudarar kauna wanda duk yakeyi ya bata

Toshe kunaye karda ki bi zancen yan zuga
Kin zamo sashen zuci babu ke sai ta buga
Kin sani koshi shi yake saka a ci a raga
Naga tuta ta zani fara in hau karaga
Mun zamo daya kin rike ni tamkar dan uwa
Ga misalai kin ginan wurare yar uwa

Kullum tunani na auren ki inyi wa maza rata
Cikar muradu na kin zama ta daban a cikin mata
Abinda ke rai na in mallake ki gimbiyar mata
Koh gobe na shirya aure muyo dake manufata
Ki bani soyayyar ki nima na baki tawa ki alkinta

Shi dan kare kin san harshe ke saka kushe shi
Duk wanda zai kawo gulmar raba mu toh ki kyale shi
Ki sa a rai lallai saye martabar ki nayi al washi
Kullum tunani na wai yaushe zani hau gadon laushi?

Mix kobincus
Mafarki na



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link