BURIN ZUCIYA

Burin zuciya
In ba ke toh akwai damuwa
Bazan barki ba
S piano on the beat

Soyayya nake yawo
Duk inda zani
Cikin jiki ta zaman ciwo
Tai mini rauni
Wa zani fada wa ya jini?
A so wa zaya dube ni?
Ko mai ya faru dani ne?
Nazam sillar sa
Tillas nai bayanin so
Dame ya kunsa

In nai wa zaya ban amsa?
Da jin muryar ki na kosa
Kin yi min sutura ta mai kyau
Na baki tsumma
Nine sanadi a soyayya kin ka fara rama
Dake ni zanyi tarayya
Rashin ki ya sa wa rai jinya
Haba sahiba?

Ni dai sai dake
Ji tausai na

Korafin zuciya yanzu wa zan fada wa ya jini?
So ya sanya ni damuwa
Wa zana yi wa bayani?
Shi so da kauna ke manta wannan
Bai duba zamani
Ya zana manta irin hallacin da kikayi mani

Ki duba Allah ki duba manzo
Ki tausaya mani
Ki duba halin da zan shiga
Ki agaza mani
Nasan da na saki yin hawaye
A kai na kin tarwatse kawaye
Nasan da cewa mene kikeyi
Ni mutuwa nike
Ki bani dama ki ban makamai na san ki in rike
Giya ta so ta saka ni maye

Na gode Allah kina a raye
Kuskure na na gane
Ke dai ki kwantar da hankali
Zuciya kin cike
Zan je na shaida wa ahali
Ki bani dama
Haba masoyiya
Ki bani dama

Ni dai sai dake
Daure, ki bani dama



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link