BABY

So na ne fa
Kauna ce ta hada mu (on the beat)
Karka biyewa masu adawa
Kece bake bata sukuni
Kasan so da wuyar sani

Kauna ce ta hada mu karki bi zancen masu adawa
Kinsan so da wuyar sani zuciya bake babu sukuni

Kauna ce ta hada mu karka bi zancen masu adawa
Kasan so da wuyar sani zuciya bakai bata sukuni
Ahh baby

A farko zanyi batun abinda yake caja mini ruhi
Sannan inyi yabo gare ki abar so, za nayi sharhi
Ke na saka raina, ba a cire mini ke wallahi
Rai dagin goro ne ruwan kauna debo sa ki bani
Ni mai son ki ne

Ina da abin cewa, tunda akan so kayi bayani
Ka zama tauraro, zuciya ba kai bata sukuni
Ka rike alkawari, baka guje min nayi yakini
In har ba kai ba, soyayyar wani mai zai kaini
Ahh baby
Ni mai sonki ne

Akwai wani labari, zo kusa sa kunnin ki kiji ni
Gaskiya ce jari, mai ita ba'a hana shi sukuni
Kibar zancen makiya don Allah ni mai zamani
Ina sauya hali a dodar zamu haye bisa tsani
Ah baby

Kai dai kayi hakuri, karda ka damu da mai maka sharri
In wani yayi sharri gun ka maida mai alkhairi
Komai da lokaci bana shiga inkari
Labarin zuciya sai fuska ta hau mizani
Karka biyewa masu adawa
Baby

Kauna ce ta hada mu karki bi zancen masu adawa
Kinsan so da wuyar sani zuciya bake babu sukuni
Kauna ce ta hada mu karka bi zancen masu adawa
Kasan so da wuyar sani zuciya bakai babu sukuni
Ahh baby



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link