RUHINA

(Sona ne fah)
Ahh
On the beat
Ahh

Ruwan zuma, a gun wasu su ruwan guba ne ashe
Ya ratsa sassa, ya shiga zuciya yayi min dashe
Da gaske ne, so na sanya zautuwa wai ashe
Idanuwa na, hasken jikin ki ya karkashe

Kibani kauna, bance ki boye sirrin ki ba
Ki sanya rai, nidai ba zana cuce ki ba
Zan bada kaina fansa kan son ki kar kiyi fargaba
Dukan masoyan dake neman ki daya bazai kaini ba

Ki kara ji, sannan ko karkade kunnuwa
Kina da kyau, shekin ki yafi tauraruwa
Da kin wuce, sai yan maza su hau faduwa
Ranar da zan samu yabo a gare ki duniya sabuwa

Ban gane so, ban gane ki kina dab dani
Rabe mini, kan so da ki, ki ganar dani
Ke malama ce, ilimi na so ki koyar dani
Buri na raina, nidai ace kina yi dani

Bana da zabi, duk inda zaki je zani je
Kasa da taki, sama'u ke aje girgije
In babu yabe, a ginin kasa yakan barbaje
Ni kin kure nawa tunani daga kan ki na sallama

Abinda da duk za'ayi kaina ba zana daina kauna ba
Idan nace in bar kauna banyi wa zuci dai-dai ba
Komai za nayi indai a kan ki ne banyi asara ba
Duk dai da nasan shi so a wani sa'in ba'a samu ba
Zan jure fama in tabbatar wa so ban sare ba
Inda bora watarana bazan gindawa ba
Taho mu zauna kiyi zantuka na so guna yar baba
Na toshe kunni bazan ji zantukan masu adawa ba

Komai ka samu karshe toh binciko shi to ai yayi mafari
Ina da burin ki a raina kinga ko kauna tayi kauri
Wutar kara bata kauna mai bidar ta sai dai yayi sauri
Ina batu na kai tsaye sam baida ni dake ba wani dari

Mai son ki ne, ni ina tabbaci
Ko munyi aure sa rai sai kinci zana ci
Ke tawa ce bake zana haukace
Zance na zuci fuska akewa tambaya



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link