DALILIN SO

(DJ Sauti on the Beat)
Dalilin so
Kaji dalilin so nima
Kujerar so
Zauna kujerar so kaima

Soyayyah ra'ayi, garin masoyi bai mini nisa ba
Kadai jani muje, muyi rabuwa ni banga dalilai ba
Kalmomin hakane, duk aiki bai zarce agogo ba
Kwarai shine mai shi, watan watarana ban fadi karya ba
Ke dai kiyi hakuri, in rufe ince sa'ar dabo
Kauna za nayi ma, sa da rai koba da kobo
Mun jure fama, tunda dai ance da rabo
Bana yin sanya, kota yaya sai na yunkura
Sai na yunkura

Tafiya da gwani dadi, son ki a rai ya zam min magani
Nagode Allah, ai fitila ce gatan lagwani
Duniya kwai fadi, rabbi kawo dogon zamani
Mun sha lahaula, ja muje ba mai yima razini
Dubi agogo na, lokaci za nayi wa adani
Suna linzami, addu'a karshen mai lahani
Zuciya kin nisa, me kike ji ke shaida mini
Ai kai dinne ne, dukka siffofin ka tattara
Ka tattara

Bake wa zanyi wa baitocin kauna da so
Yau tafiyar tamu tayi nisa ko ba'a so
A rai nake jin sirrin so zan fallaso
Nima kana nan a dama na kaine ka so
Ke zana kaiwa mahaifa na suyi min iso
Farin ciki zan yi na samo babban kaso
Mu tasa kaunar ki na gana, na gane so
Na matsu nidai muyo aure, in tattara

Duba inda guri sai in dara
Tsini ba'a gwadawa allura
Kauna dani dake yau anfara
Kodai ba'a gwadawa yar bora
Bake bani da saura in ban kaura
Niko idan nace da zan haura
Rintsa ba'a gini sai an tara
Manzo, mun ka rika abban Zahra

Musax Mix



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link