HELLO

(DJ Sauti on the beat)

Hello
Ina jinka
Ina fatan kina nan
Eh lafiya
Kin san ina son ki
Nasan da hakan ka bar yimin magiya
Shi so lalura ne duk wanda ya farwa baya jin kira
Fahimci nawa zance dani da kai jirgin zai cira
Kalubalen kauna yau ya riske mu dan sai an kara
Idan ka yada ni bazana iya ba komai zan rasa

Hello
Ina jinka

Ni bani jin cewa idan bake in zauna duniya
Abinda ke raina shine ka fadi dakai zan tutiya
Komai kika yi guna zanso wataran kiyi min fariya
Sirrin ka sirri na taya za'ayi a faifai in kasa?

Soyayyah madara, taki nasha ban kurbi ta kowa ba
Nima nayi katari, na rike kaunar gaske bazan yarba
Mai san badda kwabo zaya kashe ko bai bidi kowa ba
Kai dai kayi hakuri mai nasara bai kauce rabo nai ba
Tafiya yau tai tafiya kiyi damara dan ni nasa danba
Kashi inba tsoka bai ciyuwa inba da hakori ba
Wadan su suna magana wai haduwar mu baza tayi karko ba
Karda ka damu kawai, ni dakai bamu tsangumi kowa ba
Shi samu da rashi, rabbi yake baiwa ba kowa ba
Mai hakurin tafiya, ba zai lalace guzuri nai ba

Akwai bayanai, dake a zuciya sun dade
Zan bude sirrai, sai in dani dake mun hade
Ka ceci raina, in har ka yada dani na kade
Iya sani na, ko wacce wataran zai sude
Okay, hahhaa

Hello?

Ki bude kunnaye, in tuna miki maganar rannan
Kafin ka furta ka tuna abinda kamin a dakin nan
Ki daina sanya ni shauki domin yanzu bana nan
Idan ka dawo masoyi dole mu karkare gasa

(Musax mix)



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link