MAYAUDARIYYA

Ashe ke mayaudariya ce
Sannan makaryaciya ce, wayyo

Ashe ke mayaudariya ce
Sannan makaryaciya ce, wayyo

Idan da so da amana, na shaida ruwa bazai ci gwani ba
Alkawari kaya ne, mai kunya bazai ki saukewa ba
Na zuci na ta dakon so, ciwon banga randa zan warke ba
Wa zan fadawa yaji ni? Kauna tayi min mugun kamu, wayyo

So yayi mini danyan aiki, na afka cikin mummunar gurbi
Zuciyar mai yin so, inta kamu bata duban zabi
Shigo-shigo ba zurfi, an kayi min ana ta cemin hubbi
Niko na sawo linzami, alkawara mu kayi cika sun kasa, wayyo

Shi lokaci bako ne, ko ya zo a wataran zai shude
Kyawo ga mai ci ya raga, babban yace zai sude
Abinda banyi zato ba, shina gani a so yasa na rude
Abin yanai mini ciwo, an mini yaudara cikin soyayya, wayyo

Mayaudari zai rushe, koya tashi baya dogon zango
Gaskiya ce jari, ita na runguma ta zam mini jigo
Mai bida zai samu, muyi nazari na dashen icen rogo
Duniya labari, komai zai wuce na barwa Allah



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link