FARIN CIKI

Farin cikin rai na
Kinzamo
(Beat Amjad record)

Ashe so yan da dadi
Yana dadi haushi
Ni dai ya mini rana a rayuwata
Cikin kauyuka da birni
Idan na duba
So ya sa wandansu kuka
Maza da mata

Toh ya zanyi rabo da kai so? Bazan iya ba
Domin rabbi ya dasa ka a zuciya ta
Ki daure ki mini kauna kamar ta umma
Ki alkinta sirrika na masoyiyta
Kullum dubun mutane
Suna tunanin ya za ayi su mulki kauna su sarrafa ta

Soyayya tana da dadi
Tana da daci
Masoyi yana da rana
Yana da rana ne

A kaunar ki na dake kinga zuciya ke take jira
Idan har ina da ke ba abinda zai sa ni na tinzira
Rike min alkawari kar ziga ta sanya ki hakkura
Kalamai na gaskiya dani dake babu rabuwa
A so munzamo daya ki kara damke ni yar uwa
Na shaida wa makiya ko ina zani je dake
Kin zamto rabin jiki gare ni
Ya zana yada ke?
Na tantance zahirin takanda ai ta wuce rake
Saurare ni sahiba sa alkawar' naki ban sake

Dukkan wani ya shirin taba ki toh ya kira ruwa
Aure namu in a kai zan maki baine hawa-hawa

Abun duk da zuciya taso a bata shi baiyuwa
Ina miki gaskiyar kaunar da bata misaltuwa
Bacci nai da nazarin in baki toh zanyi zautuwa
Jini har da jijiya kaunar ki na kara hawhawa
Yawaitar farinciki shi ne yake sa ayo rawa
Kira na masoyiya ki kaurace wa ma karkawa
Alkarya ta so da kauna raka ni mai so mu zagaya
Inaji dake abar so gare ni bakya halin tsiya
Koda za a tara matan kasar mu kece sarauniya
Kina nan a rayuwata dare, maraice da safiya

Ashe zuciya tana san abunda ya so ta hakane
Domin naga zahiri kin bani kauna a bayyane
Ciwo na cikin barewa aje da Allah ki bata kanwa
Soyayya hauwayeniya mai kala-kala ja, baki da tsanwa
Wasu ta saka su hawka
Wasu sun gan gara gushewa
Dokin nata ba gwani da kayi kaudi ka dauki garwa
Masoyiya

Midget mx



Credits
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com

Link